Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 12:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma ya yi watsi da shawarar da dattawan suka ba shi, sai ya nemi shawara daga wurin matasa, tsararsa.

9. Ya ce musu, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan da suka roƙe ni wai in rage musu nawayar da tsohona ya aza musu?”

10. Matasa da suke tsara ɗaya da shi kuwa suka ce masa, “Haka za ka faɗa wa mutanen nan da suka yi magana da kai, cewa tsohonka ya nawaita musu, amma sai ka sawwaƙa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun tsohona kauri.

11. Zan ƙara a kan nawayar da tsohona ya aza muku. Shi ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunamai.’ ”

12. Yerobowam da dukan mutane suka zo wurin Rehobowam a rana ta uku kamar yadda ya faɗa musu su zo wurinsa bayan kwana uku.

13. Da suka zo, sai sarki ya yi musu magana da zafi, ya kuma yi watsi da shawarar da dattawa suka ba shi.

14. Ya yi musu magana bisa ga shawarar matasa ya ce, “Tsohona ya nawaita muku, ni kuwa zan ƙara nawaita muku. Tsohona ya yi muku horo da bulala, amma ni zan yi muku da kunamai.”

15. Haka kuwa sarki ya ƙi jin roƙon da jama'a suka yi masa, gama Ubangiji ne ya sa al'amarin ya zama haka domin ya cika maganarsa, wadda ya yi wa Yerobowam ɗan Nebat ta bakin Ahija mutumin Shilo.

16. Da mutanen Isra'ila suka ga sarki ya ƙi jin roƙonsu, sai suka yi ihu, suna cewa, “A yi ƙasa da Dawuda da iyalinsa. Me suka taɓa yi mana? Mazajen Isra'ila, bari duka mu tafi gida! Mu bar Rehobowam ya lura da kansa!”Jama'ar Isra'ila fa suka tayar,

17. suka bar Rehobowam ya sarauci jama'ar da take zaune a yankin ƙasar Yahuza.

18. Sa'an nan sarki Rehobowam ya aiki Adoniram, shugaban aikin tilas, sai mutanen Isra'ila suka jajjefe shi da duwatsu har lahira. Sarki Rehobowam kuwa ya gaggauta, ya hau karusarsa, ya tsere zuwa Urushalima.

Karanta cikakken babi 1 Sar 12