Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 12:24-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Ubangiji ya ce, “Kada ku haura zuwa yaƙi da 'yan'uwanku, mutanen Isra'ila, sai kowa ya koma gidansa, gama wannan al'amari daga wurina ne.” Su kuwa suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka koma gida.

25. Sa'an nan sarki Yerobowam ya gina Shekem a ƙasar tudu ta Ifraimu, ya zauna can. Daga can kuma ya tafi ya gina Feniyel.

26. Yerobowam kuwa ya ce a zuciyarsa, “Mulkin fa zai koma gidan Dawuda.

27. Idan mutanen nan sun ci gaba da zuwa Urushalima don miƙa wa Ubangiji hadayu, zuciyarsu za ta koma kan sarki Rehobowam, na Yahuza, za su kashe ni, su koma wurinsa.”

28. Sai sarki Yerobowam ya yi shawara, ya siffata 'yan maruƙa biyu da zinariya. Sa'an nan ya ce wa jama'arsa, “Zuwanku Urushalima ya isa, yanzu ga allolinku, ya Isra'ilawa, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar.”

29. Ya kafa siffar maraƙi ɗaya a Betel, ɗayan kuma a Dan.

30. Wannan abu ya zama zunubi, gama mutane sun tafi wurin siffofin maruƙan nan a Betel da Dan.

31. Ya kuma gina masujadai a tuddai, sa'an nan ya sa waɗansu daga cikin mutane waɗanda ba Lawiyawa ba, su zama firistoci.

32. Yerobowam kuma ya sa a yi idi ran goma sha biyar ga wata na takwas kamar yadda ake yi a Yahuza. Ya miƙa hadayu bisa bagade, haka ya yi a Betel. Ya yi ta miƙa hadayu ga siffofin maruƙan da ya yi. Ya kuma sa firistoci a masujadan da ya gina a Betel.

33. Ya tafi gaban bagaden da ya gina a Betel a rana ta goma sha biyar ga wata na takwas, wato watan da ya zaɓa don kansa. Ya kafa wa jama'ar Isra'ila idi. Sai ya tafi don ya ƙona turare a kan bagaden.

Karanta cikakken babi 1 Sar 12