Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 10:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sarauniyar Sheba ta ji labarin sunan da Sulemanu ya yi ta dalilin sunan Ubangiji, ta zo don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya.

2. Ta iso Urushalima da 'yan rakiya da yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya da yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa duk abin da yake a ranta.

3. Sulemanu ya amsa tambayoyinta dukka, ba abin da ya gagare shi amsawa.

4-5. Sarauniyar Sheba ta yi mamaki sa'ad da ta ga hikimar Sulemanu, da gidan da ya gina, da irin abincinsa, da irin zaman fādawansa, da yadda ma'aikatan gida suke hidima, da irin tufafinsu, da masu ba da abin sha, da hadayu na ƙonawa waɗanda yakan miƙa cikin Haikalin Ubangiji.

6. Sai ta ce wa Sulemanu, “Labarin da na ji a ƙasata a kan al'amuranka da hikimarka, gaskiya ne.

7. Amma ban gaskata da labarin ba, sai da na zo na gani da idona, ashe, ko rabi ma ba a faɗa mini ba, gama hikimarka da wadatarka sun fi abin da na ji.

8. Jama'arka, da fādawanka waɗanda suke tsaye a gabanka kullum, sun yi sa'a gama suna jin hikimarka.

9. Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda ya yarda da kai, ya sa ka a kan gadon sarautar Isra'ila, domin Ubangiji yana ƙaunar Isra'ila har abada, ya naɗa ka sarki domin ka zartar da shari'a da adalci.”

10. Sa'an nan Sarauniyar Sheba ta ba sarki talanti ɗari da ashirin na zinariya,da kayan yaji mai yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa kamar yadda Sarauniyar Sheba ta kawo wa sarki Sulemanu ba.

11. Bayan wannan kuma jiragen ruwa na Hiram da suka kawo zinariya daga Ofir, sun kuma kawo itacen almug da yawa, da duwatsu masu daraja daga can.

12. Da itacen almug ne sarki ya yi ginshiƙai na Haikalin Ubangiji da gidan sarki, ya kuma yi molaye da garayu domin mawaƙa. Har wa yau ba a taɓa samu, ko ganin irin itacen almug kamar wannan ba.

13. Sarki Sulemanu ya ba Sarauniyar Sheba duk abin da ta nuna tana bukata, banda kyautar karamcin da ya yi mata. Sai ta koma ƙasarta tare da barorinta.

14. Yawan zinariya da akan kawo wa Sulemanu kowace shekara yakan kai talanti ɗari shida da sittin da shida na zinariya.

15. Banda wanda ya sa wa 'yan kasuwa, da fatake, da harajin dukan sarakunan Arabiya, da na hakimai.

Karanta cikakken babi 1 Sar 10