Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 1:30-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. a yau ne kuma zan cika alkawarin da na yi miki da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila, cewa Sulemanu, ɗanki, zai yi mulki a bayana, shi ne zai hau gadon sarautata ya gāje ni, haka kuwa zan yi yau.”

31. Bat-sheba kuwa ta rusuna har ƙasa, domin girmamawa, ta ce, “Ran ubangijina sarki ya daɗe har abada!”

32. Sarki Dawuda kuma ya ce, “Ku kirawo mini Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada.” Su kuwa suka zo gaban sarki,

33. ya ce musu, “Ku tafi tare da fādawana, ku sa Sulemanu, ɗana, ya hau alfadarina, ku kai shi Gihon,

34. a can Zadok firist, da annabi Natan za su zuba masa mai, ya zama sarkin Isra'ila, sa'an nan ku busa ƙaho, ku ce, ‘Ran sarki Sulemanu ya daɗe.’

35. Sa'an nan ku zo da shi ya hau gadon sarautata, gama shi ne zai zama sarki a maimakona. Na sa shi ya zama mai mulkin Isra'ila da Yahuza.”

36. Sai Benaiya ɗan Yehoyada ya ce wa sarki, “Za a yi haka, Ubangiji Allah na ubangijina, sarki, ya tabbatar da haka.

37. Kamar yadda Ubangiji ya kasance tare da ubangijina, sarki, haka kuma ya kasance tare da Sulemanu, ya fifita gadon sarautarsa fiye da na ubangijina, sarki Dawuda!”

38. Saboda haka sai Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada, da masu tsaron lafiyar sarki, suka tafi, suka sa Sulemanu ya hau alfadarin sarki Dawuda. Suka kuma kai shi Gihon.

39. A can ne Zadok, firist, ya ɗauki ƙahon mai wanda ya kawo daga alfarwa ta sujada, ya zuba wa Sulemanu. Sa'an nan suka busa ƙaho, dukan mutane kuwa suka ce, “Ran sarki Sulemanu ya daɗe.”

Karanta cikakken babi 1 Sar 1