Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 1 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Abishag ta Yi wa Dawuda Hidima

1. Sarki Dawuda ya tsufa ƙwarai, don haka ko an rufe shi da abin rufa ba ya jin ɗumi.

2. Saboda haka fādawansa suka ce masa, “Ranka ya daɗe bari mu nemo maka budurwa, wadda za ta zauna tare da kai, ta riƙa yin maka hidima, ta kwanta a ƙirjinka don ka riƙa jin ɗumi.”

3. Suka kuwa nemi kyakkyawar yarinya a dukan ƙasar Isra'ila. Sai suka sami Abishag a Shunem, suka kawo ta wurin sarki.

4. Ko da yake yarinyar kyakkyawa ce ƙwarai, ta zama mai lura da sarki, ta kuwa yi masa hidima, amma sarki bai yi jima'i da ita ba.

Adonija Ya Ci Sarauta

5. Adonija, dan da Haggit ta haifa wa Dawuda, ya ɗaukaka kansa cewa, “Zan zama sarki.” Ya kuwa shirya wa kansa karusai, da dakarai, da zagage hamsin a gabansa.

6. Tsohonsa bai taɓa tsawata masa ba. Shi kuma mutum ne kyakkyawa, an haife shi bayan Absalom.

7. Ya gama baki da Yowab ɗan Zeruya, da Abiyata, firist. Su kuwa suka yarda su goyi bayansa, su taimake shi.

8. Amma Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da annabi Natan, da Shimai, da Reyi, da masu tsaron lafiyar Dawuda, ba su goyi bayan Adonija ba.

9. Adonija kuwa ya yi hadaya da tumaki, da bijimai, da turkakkun dabbobi kusa da Dutsen Zohelet, wato dutsen maciji, wanda yake gab da Enrogel. Ya gayyaci dukan 'yan'uwansa, 'ya'yan sarki, da fādawan da suke a Yahuza.

10. Amma bai gayyaci annabi Natan, ko Benaiya, ko masu tsaron lafiyar sarki, ko Sulemanu ɗan'uwansa ba.

An Zaɓi Sulemanu Ya Zama Sarki

11. Natan kuwa ya ce wa Bat-sheba tsohuwar Sulemanu, “Ba ki ji cewa Adonija ɗan Haggit ya zama sarki ba? Sarki Dawuda kuma bai sani ba!

12. Yanzu sai ki zo in ba ki shawara domin ki tsira da ranki da na ɗanki Sulemanu.

13. Ki tafi wurin sarki Dawuda, ki ce masa, ‘Ran sarki ya daɗe, ashe, ba ka rantse mini ba cewa, Sulemanu ɗana zai yi mulki bayanka, shi ne kuma zai hau gadon sarautarka? Me ya sa Adonija ya zama sarki?’

14. Sa'ad da kike magana da sarki, ni ma zan shigo in tabbatar da maganarki.”

15. Bat-sheba kuwa ta tafi wurin sarki a ɗakinsa. Sarki dai ya tsufa ƙwarai, Abishag, yarinyar nan daga Shunem, tana yi masa hidima.

16. Bat-sheba ta rusuna, ta gai da sarki. Sai sarki ya ce mata, “Me kike so?”

17. Ta ce masa, “Ranka ya daɗe, ka riga ka rantse mini da sunan Ubangiji Allahnka, ka ce, ‘Sulemanu ɗanki zai yi mulki bayana, shi ne zai hau gadon sarautata.’

18. To, ga shi Adonija ya zama sarki, ko da yake kai ba ka sani ba.

19. Ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Abiyata firist, da Yowab shugaban sojoji, amma bai gayyaci Sulemanu ɗanka ba.

20. Ranka ya daɗe, yanzu idanun dukan jama'ar Isra'ila suna kallonka don su ga wanda za ka nuna musu ya gāji gadon sarauta a bayanka.

21. In ba haka ba, zai zama sa'ad da ka rasu za a ɗauka ni da ɗana, sulemanu, masu laifi ne.”

22. Tana cikin magana da sarki, sai annabi Natan ya zo.

23. Aka faɗa wa sarki cewa, ga annabi Natan. Da ya zo gaban sarki, sai ya rusuna ya gaishe shi.

24. Sa'an nan ya ce, “Ranka ya daɗe, ashe, ko ka sanar, cewa Adonija ne zai gaje ka?

25. Gama yau ɗin nan ya tafi ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Yowab shugaban sojoji, da Abiyata firist. Ga shi, suna ci suna sha tare da shi, suna cewa, ‘Ran sarki Adonija ya daɗe.’

26. Amma ni da Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da ɗanka Sulemanu, bai gayyace mu ba.

27. Ranka ya daɗe ko ka tabbatar da haka, amma ba ka ko faɗa wa fādawanka, cewa ga wanda zai gāje ka ba?”

An Naɗa Sulemanu Sarki

28. Sai sarki Dawuda ya ce, “A kirawo mini Bat-sheba.” Ta kuwa zo gaban sarki.

29. Sa'an nan ya ce mata, “Na yi miki alkawari da Ubangiji mai rai wanda ya fanshe ni daga dukan wahala,

30. a yau ne kuma zan cika alkawarin da na yi miki da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila, cewa Sulemanu, ɗanki, zai yi mulki a bayana, shi ne zai hau gadon sarautata ya gāje ni, haka kuwa zan yi yau.”

31. Bat-sheba kuwa ta rusuna har ƙasa, domin girmamawa, ta ce, “Ran ubangijina sarki ya daɗe har abada!”

32. Sarki Dawuda kuma ya ce, “Ku kirawo mini Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada.” Su kuwa suka zo gaban sarki,

33. ya ce musu, “Ku tafi tare da fādawana, ku sa Sulemanu, ɗana, ya hau alfadarina, ku kai shi Gihon,

34. a can Zadok firist, da annabi Natan za su zuba masa mai, ya zama sarkin Isra'ila, sa'an nan ku busa ƙaho, ku ce, ‘Ran sarki Sulemanu ya daɗe.’

35. Sa'an nan ku zo da shi ya hau gadon sarautata, gama shi ne zai zama sarki a maimakona. Na sa shi ya zama mai mulkin Isra'ila da Yahuza.”

36. Sai Benaiya ɗan Yehoyada ya ce wa sarki, “Za a yi haka, Ubangiji Allah na ubangijina, sarki, ya tabbatar da haka.

37. Kamar yadda Ubangiji ya kasance tare da ubangijina, sarki, haka kuma ya kasance tare da Sulemanu, ya fifita gadon sarautarsa fiye da na ubangijina, sarki Dawuda!”

38. Saboda haka sai Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada, da masu tsaron lafiyar sarki, suka tafi, suka sa Sulemanu ya hau alfadarin sarki Dawuda. Suka kuma kai shi Gihon.

39. A can ne Zadok, firist, ya ɗauki ƙahon mai wanda ya kawo daga alfarwa ta sujada, ya zuba wa Sulemanu. Sa'an nan suka busa ƙaho, dukan mutane kuwa suka ce, “Ran sarki Sulemanu ya daɗe.”

40. Mutane duka kuwa suka bi shi, suna bushe-bushe, suna murna da yawa, kamar ƙasa ta tsage saboda sowarsu.

41. Adonija da dukan baƙin da suke tare da shi suka ji amon sowa bayan da suka gama cin abinci. Da Yowab ya ji busar ƙaho, sai ya ce, “Mene ne dalilin wannan hargitsi a birni?”

42. Yana cikin magana ke nan sai ga Jonatan ɗan Abiyata, firist, ya zo. Adonija ya ce musu, “Shigo, gama kai nagarin mutum ne, ka kawo albishir.”

43. Jonatan kuwa ya ce wa Adonija, “A'a, gama ubangijinmu, sarki Dawuda, ya naɗa Sulemanu sarki.

44. Sarki ya aiki Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada, da masu tsaron lafiyar sarki. Su kuwa suka sa Sulemanu ya hau alfadarin sarki.

45. Zadok firist, da annabi Natan kuma suka zuba masa mai a Gihon don ya zama sarki. Daga can suka tashi da murna don haka ake hayaniya a birnin. Wannan ita ce hayaniyar da kake ji.

46. Sulemanu ne sarki yanzu.

47. Banda wannan kuma, fādawa sun tafi su kai caffa ga sarki Dawuda, suna cewa, ‘Allahnka ya sa Sulemanu ya yi suna fiye da kai, ya kuma fīfita gadon sarautarsa fiye da naka.’ Sai sarki ya sunkuyar da kansa a gadonsa.

48. Sa'an nan ya ce, ‘Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra'ila wanda ya sa ɗaya daga cikin zuriyata ya hau gadon sarautata yau, idona kuwa ya gani.’ ”

49. Sai baƙin Adonija duka suka tashi suna rawar jiki, kowa ya kama hanyarsa.

50. Adonija kuwa ya ji tsoron Sulemanu, sai ya tashi, ya tafi, ya kama zankayen bagade.

51. Aka faɗa wa Sulemanu cewa ga Adonija yana jin tsoron sarki Sulemanu, gama, ga shi, ya kama zankayen bagade, yana cewa, “Bari sarki Sulemanu ya rantse mini tukuna, cewa ba zai kashe ni ba.”

52. Sulemanu kuwa ya ce, “Idan ya nuna kansa nagarin mutum ne, ko gashin kansa guda ɗaya ba zai faɗi ƙasa ba, amma idan aka iske shi da mugunta, to, lalle kashe shi za a yi.”

53. Sarki Sulemanu kuwa ya aika aka kawo shi daga bagaden. Da ya zo, sai ya rusuna, ya gai da sarki Sulemanu. Sulemanu ya ce masa, “Tafi gidanka.”