Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 9:15-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ana gobe Saul zai tafi wurin Sama'ila, Ubangiji ya bayyana wa Sama'ila.

16. Ya ce masa, “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sai ka zuba masa mai, ka keɓe shi sarki bisa jama'ata Isra'ila. Zai ceci jama'ata daga hannun Filistiyawa, gama na ga azabar da jama'ata suke sha, gama na ji kukansu.”

17. Da Sama'ila ya ga Saul, sai Ubangiji ya ce masa, “To, ga mutumin da na faɗa maka! Shi ne wanda zai sarauci jama'ata.”

18. Sa'an nan Saul ya tafi wurin Sama'ila a ƙofar gari, ya tambaye shi, “Ina gidan maigani?”

19. Sama'ila ya amsa ya ce, “Ni ne maiganin, wuce gaba, mu tafi wurin yin sujada a kan tudu, gama yau dukanku za ku ci abinci tare da ni. Gobe da safe zan amsa muku dukan tambayoyinku, sa'an nan in sallame ku.

20. A kan zancen jakunanku da suka ɓace yau kwana uku ke nan da suka wuce, kada ka damu, gama an same su. Banda wannan ma, ga wa Isra'ilawa duka suke sa zuciya? Ba kai ba ne da gidan mahaifinka?”

21. Saul ya ce, “Ni mutumin kabilar Biliyaminu ne, kabilar da ta fi ƙanƙanta a Isra'ila. Iyalina kuma su ne mafi ƙanƙanta a iyalan kabilar Biliyaminu. Me ya sa ka faɗa mini irin wannan magana?”

22. Sa'an nan Sama'ila ya shigar da Saul da baransa a babban ɗakin taruwa, ya sa su zauna gaba inda baƙi suke, wajen mutum talatin aka gayyata.

23. Sama'ila kuwa ya ce wa mai dahuwa, “Kawo naman nan da na ba ka, wanda na ce ka ajiye shi dabam.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 9