Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 5:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ubangiji kuwa ya hukunta mutanen Ashdod ƙwarai da gaske, ya kuma razanar da su, ya azabtar da su da marurai, su da na kewaye da su.

7. Da mutanen Ashdod suka ga yadda abin yake, sai suka ce, “Kada a bar akwatin alkawarin Allah na Isra'ila tare da mu, gama ya tsananta mana, mu da Dagon, allahnmu.”

8. Sai suka aika, aka kirawo dukan sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka ce musu, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila?”Suka ce, “Sai a kai shi Gat.” Su kuwa suka kai shi can.

9. Amma da suka kai shi can sai Ubangiji ya hukunta birnin, ya gigita su, ya yi musu azaba da marurai, yara da manya.

10. Sai suka kai akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron. Amma da aka kai shi Ekron, sai mutanen Ekron suka fashe da kuka, suka ce, “Sun kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra'ila don ya kashe dukanmu.”

11. Suka kuma aika a kirawo sarakunan Filistiyawa, suka ce, “Ku aika da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila zuwa inda ya fito don kada ya kashe mu duk da iyalinmu.” Dukan birnin ya gigita ƙwarai, gama Ubangiji yana hukunta su da tsanani.

12. Marurai sun fito wa mutanen da ba su mutu ba, mutane suka yi kuka domin allolinsu su cece su.

Karanta cikakken babi 1 Sam 5