Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 4:16-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Mutumin ya ce wa Eli, “Yau daga wurin yaƙin na tsere, na gudo gida.”Eli ya ce, “Dana, me ya faru?”

17. Sai wanda ya kawo labarin ya ce, “Isra'ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, an kashe mutane da yawa, har ma da 'ya'yanka biyu, Hofni da Finehas, sun rasu, an kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

18. Da aka ambaci akwatin alkawari, sai Eli ya tuntsura da baya daga inda yake zaune a bakin ƙofar gari, wuyansa kuwa ya karye, ya mutu, gama shi tsoho ne, mai ƙiba. Ya shekara arba'in yana shugabancin Isra'ila.

19. Surukar Eli, matar Finehas, tana da juna biyu, ta kusa haihuwa. Sa'ad da ta ji labari an ƙwace akwatin alkawarin Allah, surukinta kuma da mijinta sun rasu, sai ta kama naƙuda farat ɗaya, ta haihu.

20. Tana bakin mutuwa, matan kuwa da take taimakonta suka ce mata, “Ki yi ƙarfin hali, gama kin haifi ɗa namiji.” Amma ba ta amsa ba, ba ta kuma kula ba.

21. Sai ta sa wa yaron suna Ikabod, wato ɗaukaka ta rabu da Isra'ila domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma surukinta da mijinta sun rasu.

22. Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra'ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 4