Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 30:5-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. An kwashe matan Dawuda biyu ganima, wato Ahinowam Bayezreyeliya da Abigail Bakarmeliya, matar Nabal wanda ya mutu.

6. Dawuda kuwa ya damu ƙwarai gama mutane suna niyyar su jajjefe shi da duwatsu, domin ransu ya ɓace saboda 'ya'yansu mata da maza. Amma Ubangiji Allahnsa ya ƙarfafa shi.

7. Sai ya ce wa Abiyata firist, ɗan Ahimelek, ya kawo masa falmaran. Abiyata kuwa ya kawo masa.

8. Sai Dawuda ya yi tambaya ga Ubangiji ya ce, “In bi sawun 'yan harin nan? Zan ci musu?”Ya ce masa, “Bi su, gama za ka ci musu, ka ƙwato abin da suka kwashe.”

9-10. Sai Dawuda da mutanensa ɗari shida suka tashi, suka kama hanya, suka kai rafin Besor inda suka bar mutum metan waɗanda suka kāsa. Amma Dawuda da mutum ɗari huɗu suka ci gaba da bin mutanen.

11. Mutanen Dawuda suka sami wani Bamasare a karkara, suka kawo shi wurin Dawuda. Suka ba shi abinci da ruwa, ya ci ya sha.

12. Suka kuma ba shi kauɗar ɓaure da nonnan inabi biyu. Da ya ci sai ya wartsake, gama ya yi yini uku da dare uku ba ci ba sha.

13. Dawuda kuwa ya tambaye shi, “Wane ne ubangidanka? Daga ina ka fito?”Ya amsa, ya ce, “Ni saurayi ne, Bamasare, baran wani Ba'amaleke. Kwana uku ke nan da ubangidana ya tafi ya bar ni a baya saboda ba ni da lafiya.

14. Mun kai hari a Negeb ta Keretiyawa ta Yahuza, da Negeb ta Kalibu, muka kuma ƙone Ziklag.”

15. Dawuda ya ce masa, “Za ka yarda ka kai ni wurin maharan nan?”Sai ya ce wa Dawuda, “Idan ka rantse mini da Allah, ba za ka kashe ni ba, ba kuwa za ka mai da ni wurin ubangidana ba, sai in kai ka inda maharan nan suke.”

16. Ya kai Dawuda a wurinsu, sai ga su nan a baje ko'ina a ƙasar, suna ci, suna sha, suna rawa, saboda ganima mai yawa da suka kwashe daga ƙasar Filistiyawa da ƙasar Yahuza.

Karanta cikakken babi 1 Sam 30