Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 3:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yaron nan Sama'ila yana yi wa Ubangiji aiki a hannun Eli. A lokacin nan Ubangiji bai cika yin magana da mutane ba, ba safai kuma ake samun wahayi ba.

2. Wata rana da dare Eli wanda ya kusa makancewa har ba ya iya gani sosai, yana kwance a masujada.

3. Fitilar Ubangiji kuwa tana ci. Sama'ila kuma yana kwance a masujada inda akwatin alkawarin Allah yake.

4. Ubangiji kuwa ya kira Sama'ila. Sama'ila ya ce, “Na'am.”

5. Ya sheƙa zuwa wurin Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”Amma Eli ya ce masa, “Ban kira ka ba, koma ka kwanta.” Sai Sama'ila ya koma ya kwanta.

6. Ubangiji ya sāke kiran Sama'ila. Sama'ila ya tashi ya tafi wurin Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”Amma Eli ya ce, “Ban kira ka ba, ɗana koma ka kwanta.”

7. (Sama'ila dai bai san Ubangiji ba tukuna, gama Ubangiji bai riga ya fara magana da shi ba.)

8. Ubangiji kuma ya kira Sama'ila sau na uku. Sai kuma Sama'ila ya tashi ya nufi Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”Sa'an nan Eli ya gane Ubangiji ne yake kiran yaron,

Karanta cikakken babi 1 Sam 3