Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 25:28-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Ina roƙonka ka gafarta mini laifina. Ubangiji zai sa ka zama sarki, kai da zuriyarka, kana yin yaƙi na Ubangiji. Ba kuwa za ka aikata wani mugun abu ba a dukan kwanakinka.

29. Idan wani ya tashi tsaye don ya bi sawunka, ya kuma nemi ranka, Ubangiji zai kiyaye ranka, amma rayukan maƙiyanka za a wurga su kamar dutsen majajjawa.

30. Sa'ad da Ubangiji ya cika maka dukan alherin da ya yi maka alkawari, ya kuma naɗa ka Sarkin Isra'ila,

31. ba kuwa za ka sami dalilin baƙin ciki ba, ko damuwar lamiri domin ba ka da alhakin jini, ba ka kuma ɗaukar wa kanka fansa. Sa'ad da Ubangiji ya nuna maka alheri, sai ka tuna da ni, baiwarka.”

32. Sa'an nan Dawuda ya ce wa Abigail, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda ya aike ki ki tarye ni.

33. Basirarki mai albarka ce, ke kuma mai albarka ce, gama kin hana ni zubar da jini da ɗaukar wa kaina fansa yau.

34. Hakika, Ubangiji Allah na Isra'ila ya hana in yi miki ɓarna. Da ba domin kin yi hanzari, kin zo, kin tarye ni ba, da ba wani mutumin Nabal da zai ragu kafin gobe da safe.”

35. Sai Dawuda ya karɓi abin da ta kawo masa. Ya ce mata, “Ki koma gida kada ki damu. Zan yi abin da kike bukata.”

36. Abigail ta koma wurin Nabal, ta iske shi yana biki irin na sarakuna a gidansa. Ya yi ta nishaɗi, ya bugu sosai, don haka ba ta ce masa kome ba sai da safe.

37. Da safe, sa'ad da ruwan inabi ya sake shi, sai Abigail ta faɗa masa abin da ya faru. Zuciyarsa kuwa ta tsinke gaba ɗaya.

38. Bayan kwana goma sai Ubangiji ya bugi Nabal, ya mutu.

39. Sa'ad da Dawuda ya ji Nabal ya mutu, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya sāka mini a kan irin rainin da Nabal ya yi mini. Ya kuma hana ni aikata mugunta. Ya ɗora wa Nabal muguntarsa a kansa.”Sa'an nan Dawuda ya aika, ya nemi Abigail ta zama matarsa.

Karanta cikakken babi 1 Sam 25