Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 25:18-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Sai Abigail ta yi sauri, ta ɗauki malmalar abinci guda metan, da salkar ruwan inabi biyu, da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu uku, da nonnan 'ya'yan inabi guda ɗari, da kauɗar ɓaure guda metan, ta labta wa jakai.

19. Ta ce wa samarin, “Ku yi gaba, ga ni nan tafe bayanku.” Amma ba ta faɗa wa Nabal, mijinta ba.

20. Tana tafiya a kan jaki, ta kai gindin wani dutse ke nan, sai ga Dawuda da mutanensa tafe. Ta tafi, ta sadu da su.

21. Dawuda ya ce a ransa, “Ashe, a banza ne na yi ta lura da dukan abin da yake na mutumin nan a jeji, har ba abin da yake nasa da ya ɓace. Ga shi, ya rama mini alheri da mugunta.

22. Allah ya buge ni in mutu, idan na bar masa wani mutum da rai kafin gobe da safe.”

23. Da Abigail ta ga Dawuda, sai ta yi sauri ta sauka daga kan jakin, ta durƙusa gabansa har ƙasa.

24. Ta faɗi a ƙafafunsa, ta ce, “Ya shugabana, bari laifin ya zama nawa. Ina roƙonka ka bar baiwarka ta yi magana, ka kuma yarda ka ji maganar baiwarka.

25. Kada maigidana ya kula da Nabal, gama wawa ne, kamar yadda sunansa yake, wato wawa. Ni dai ban ga samarin da ubangijina ya aika ba.

26. Yanzu, ya maigida, na rantse da ran Ubangiji da kuma ranka, ka ga Ubangiji ya hana ka zubar da jini, da ɗaukar wa kanka fansa, sai ka bar maƙiyanka da waɗanda suke nema su cuce ka su zama kamar Nabal.

27. Idan ka yarda ka karɓi kyautan nan da baiwarka ta kawo maka domin a ba samarin da suke tare da kai.

Karanta cikakken babi 1 Sam 25