Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 22:17-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Ya ce wa matsara da suke tsaye kewaye da shi, “Ku fāɗa wa firistocin Ubangiji, ku kashe su gama suna goyon bayan Dawuda, ga shi, sun sani ya gudu, amma ba su faɗa mini ba.” Amma barorin sarki ba su yarda su fāɗa wa firistocin Ubangiji ba.

18. Sa'an nan sarki ya ce wa Doyeg, “Kai ka fāɗa wa firistocin.” Sai Doyeg, mutumin Edom, ya faɗa wa firistocin, ya kashe mutum tamanin da biyar waɗanda suke saye da falmaran na lilin a wannan rana.

19. Ya kuma hallaka Nob birnin firistoci, ya kashe dukan mata, da maza, da yara, da jarirai, da shanu, da jakai, da tumaki.

20. Amma Abiyata ɗaya daga cikin 'ya'yan Ahimelek, ɗan Ahitub, ya tsere, ya gudu zuwa wurin Dawuda.

21. Sai ya faɗa wa Dawuda Saul ya kashe firistocin Ubangiji.

22. Dawuda kuwa ya ce wa Abiyata, “A ran nan Doyeg, mutumin Edom, yana wurin, na sani lalle zai faɗa wa Saul. Ni na zama sanadin mutuwar dukan mutanen gidan mahaifinka.

23. Sai ka zauna tare da ni, kada ka ji tsoro, gama wanda yake neman raina yana neman naka. Ka yi zamanka lafiya tare da ni.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 22