Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 21:8-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Dawuda kuwa ya ce wa Ahimelek, “Kana da mashi ko takobi a nan kusa? Gama ban zo da takobina ko wani makami ba, domin ka sani sha'anin sarki na gaggawa ne.”

9. Firist ya ce, “Ga takobin Goliyat, Bafiliste wanda ka kashe a kwarin Ila, a naɗe da zane a bayan falmaran. Idan kana so ka ɗauka, sai ka ɗauka, gama banda shi, ba wani takobi a nan.”Dawuda kuwa ya ce, “Ai, ba wanda ya fi wannan, sai ka ba ni shi.”

10. Sai Dawuda ya tashi, yana gudu ke nan daga wurin Saul. Ya tafi wurin Akish, Sarkin Gat.

11. Fādawan Akish kuwa suka ce masa, “Ashe, wannan ba shi ne Dawuda, sarkin ƙasar ba? Ba a kansa suka raira waƙa cikin raye-rayensu suna cewa, ‘Saul ya kashe dubbai, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai’?”

12. Da Dawuda ya ji waɗannan maganganu, sai ya tsorata ƙwarai da Akish Sarkin Gat.

13. Ya mai da kansa kamar mahaukaci a gabansa. Ya yi zane-zane a ƙyamaren ƙofofin garin. Ya bar yau na bin gemunsa.

Karanta cikakken babi 1 Sam 21