Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 20:31-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Muddin ɗan Yesse na da rai a duniya, ba za ka kahu ba. Sarautarka kuma ba za ta kahu ba. Yanzu sai ka je ka taho mini da shi. Dole kashe shi za a yi.”

32. Jonatan ya ce wa mahaifinsa, “Me ya sa za a kashe shi? Me ya yi?”

33. Sai Saul ya jefe shi da mashi don ya kashe shi. Sai Jonatan ya gane lalle mahaifinsa ya yi niyya ya kashe Dawuda.

34. Sai Jonatan ya tashi da fushi daga wurin cin abinci, bai ci abinci a rana ta biyu ga watan ba, saboda baƙin ciki a kan Dawuda, domin kuma mahaifinsa ya kunyata shi.

35. Da safe Jonatan ya tafi saura tare da wani yaro daidai lokacin da ya shirya da Dawuda.

36. Sai ya ce wa yaron, “Yi gudu, ka nemo kiban da zan harba.” Sa'ad da yaron ya ruga, sai ya harba kibiya gaba da shi.

37. Da yaron ya kai inda Jonatan ya harba kibiyar, sai ya ce masa, “Ba kibiyar tana a gaban ka ba?”

38. Ya ce wa yaron ya yi maza, kada ya tsaya. Sai yaron ya kwashe kiban ya kawo masa.

39. Amma yaron bai san abin da ake nufi ba. Jonatan da Dawuda kaɗai suka san abin da ake ciki.

40. Sa'an nan Jonatan ya ba yaron makamansa, ya ce masa, “Kai su gari.”

41. Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsun, ya rusuna har sau uku. Sa'an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, amma Dawuda ya fi yi.

42. Jonatan ya ce wa Dawuda, “Sai ka tafi lafiya, tun da yake mun riga mun rantse wa juna da sunan Ubangiji cewa, ‘Ubangiji zai zama shaida tsakanina da kai, da tsakanin zuriyarmu har abada.’ ” Dawuda ya yi tafiyarsa, Jonatan kuwa ya koma gari.

Karanta cikakken babi 1 Sam 20