Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 20:22-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Amma idan na ce wa yaron, ‘Duba, kiban suna a gabanka,’ To, ka tafi, gama Ubangiji ya sallame ka, ka tafi.

23. A kan alkawarin da muka yi, ni da kai kuwa, Ubangiji shi ne shaida a tsakaninmu har abada.”

24. Dawuda ya ɓuya a saura. A ranar amaryar wata kuwa sarki ya zauna domin cin abinci.

25. Ya zauna inda ya saba zama kusa da bango. Jonatan ya zauna daura da shi, Abner kuwa ya zauna kusa da Saul, amma ba kowa a wurin zaman Dawuda.

26. Saul kuwa bai ce kome a wannan rana ba, gama ya zaci wani abu ya sami Dawuda, kila ba shi da tsarki, lalle kam Dawuda ba shi da tsarki.

27. Amma kashegari, wato rana ta biyu ta amaryar watan, ba kowa kuma wurin zaman Dawuda, sai Saul ya ce wa Jonatan, ɗansa, “Me ya sa ɗan Yesse bai zo wurin cin abinci ba, jiya da yau?”

28. Jonatan ya ce masa, “Dawuda ya roƙe ni da naciya in bar shi ya tafi Baitalami.

29. Ya ce mini, ‘In ka yarda ka bar ni in tafi, gama a gidanmu ana ba da sadaka a gari, ɗan'uwana kuwa ya umarce ni in je. Idan na sami tagomashi a wurinka ka bar ni in tafi in ga 'yan'uwana.’ Abin da ya sa bai zo ba ke nan.”

30. Sai Saul ya husata da Jonatan, ya ce masa, “Kai yaron banza ne, mai ƙin ji, ai, na sani kana goyon bayan ɗan Yesse don ka wulakantar da kanka da mahaifiyarka.

31. Muddin ɗan Yesse na da rai a duniya, ba za ka kahu ba. Sarautarka kuma ba za ta kahu ba. Yanzu sai ka je ka taho mini da shi. Dole kashe shi za a yi.”

32. Jonatan ya ce wa mahaifinsa, “Me ya sa za a kashe shi? Me ya yi?”

33. Sai Saul ya jefe shi da mashi don ya kashe shi. Sai Jonatan ya gane lalle mahaifinsa ya yi niyya ya kashe Dawuda.

34. Sai Jonatan ya tashi da fushi daga wurin cin abinci, bai ci abinci a rana ta biyu ga watan ba, saboda baƙin ciki a kan Dawuda, domin kuma mahaifinsa ya kunyata shi.

35. Da safe Jonatan ya tafi saura tare da wani yaro daidai lokacin da ya shirya da Dawuda.

36. Sai ya ce wa yaron, “Yi gudu, ka nemo kiban da zan harba.” Sa'ad da yaron ya ruga, sai ya harba kibiya gaba da shi.

37. Da yaron ya kai inda Jonatan ya harba kibiyar, sai ya ce masa, “Ba kibiyar tana a gaban ka ba?”

38. Ya ce wa yaron ya yi maza, kada ya tsaya. Sai yaron ya kwashe kiban ya kawo masa.

Karanta cikakken babi 1 Sam 20