Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 20:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'an nan Dawuda ya gudu daga Nayot ta Rama, ya zo wurin Jonatan, ya ce masa, “Me na yi? Mene ne laifin da na yi wa mahaifinka da yake so ya kashe ne?”

2. Jonatan ya ce masa, “Allah ya sawwaƙa, ba za a kashe ka ba, gama babana yakan faɗa mini kome, ƙarami ko babba, kafin ya aikata. To, me zai sa babana ya ɓoye mini wannan? Wannan ba haka yake ba.”

3. Amma Dawuda ya rantse masa, ya ce, “Mahaifinka ya hakikance na sami tagomashi a wurinka, domin haka ba zai sanar maka da wannan ba, don kada ya baƙanta maka rai. Na rantse da Ubangiji da kai kuma, mataki ɗaya yake tsakanina da mutuwa!”

4. Sai Jonatan ya ce wa Dawuda, “Duk abin da ka ce, zan yi maka.”

5. Dawuda kuwa ya ce masa, “Ga shi, gobe ce amaryar wata, dole ne in zauna tare da sarki a teburinsa. Ka bar ni in tafi in ɓuya a saura har kwana uku.

6. Idan mahaifinka bai gan ni ba, sai ka ce masa, ni na roƙe ka ka bar ni in gaggauta zuwa Baitalami, garinmu, domin akwai ba da sadaka ta shekara saboda dukan gidanmu.

7. Idan ka ji ya ce, ‘Da kyau,’ to, baranka zai tsira ke nan, amma idan ya husata, to, sai ka sani yana niyyar kashe ni ke nan,

8. kai kuwa ka nuna mini alheri, gama ka yi mini alkawari mai ƙarfi. Amma idan ina da laifi, sai ka kashe ni da kanka. Don me za ka bar mahaifinka ya kashe ni?”

9. Jonatan ya masa ya ce, “Allah ya sawwaƙe! Da na sani babana yana da nufi ya yi maka mugunta, ai, da na faɗa maka.”

10. Sa'an nan Dawuda ya ce wa Jonatan, “Wane ne zai faɗa mini idan mahaifinka ya amsa maka da fushi?”

11. Jonatan kuwa ya ce masa, “Zo mu tafi saura.” Sai su biyu suka tafi saura.

12. Sa'an nan Jonatan ya ce wa Dawuda, “Ubangiji Allah na Isra'ila zai zama shaida. Gobe war haka, ko jibi zan tattauna maganar da mahaifina, idan da nufin alheri zuwa gare ka, zan aika, in faɗa maka.

Karanta cikakken babi 1 Sam 20