Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 17:50-58 Littafi Mai Tsarki (HAU)

50. Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara da Bafilisten. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.

51. Sa'an nan ya sheƙa zuwa wurin Bafilisten, ya zare takobin Bafilisten daga kubensa, ya datse masa kai da shi.Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka gudu.

52. Mutanen Isra'ila da na Yahuza suka tashi suka runtumi Filistiyawa, suna ihu, har zuwa Gat da ƙofofin Ekron. Filistiyawan da aka yi wa rauni suka yi ta faɗuwa a hanya tun daga Shayarim, har zuwa Gat da Ekron.

53. Da Isra'ilawa suka komo daga runtumar Filistiyawa, suka wāshe sansanin Filistiyawa.

54. Dawuda kuwa ya ɗauki kan Bafilisten ya kawo Urushalima, amma ya ajiye kayan yaƙin Bafilisten a alfarwarsa.

55. Sa'ad da Saul ya ga Dawuda ya tafi ya yi yaƙi da Goliyat, ya ce wa Abner, sarkin yaƙinsa, “Abner, ɗan wane ne wannan saurayi?”Abner ya amsa, ya ce, “Ranka ya daɗe, ya sarki, ban sani ba.”

56. Sai ya ce, “Ka tambaya mini, wane ne uban saurayin nan.”

57. Da Dawuda ya komo daga kisan Goliyat, sai Abner ya kai shi wurin Saul, Dawuda yana ɗauke da kan Bafilisten.

58. Saul ya tambayi Dawuda, ya ce, “Saurayi, kai ɗan wane ne?”Dawuda ya amsa, ya ce, “Ni ɗan baranka ne, Yesse, mutumin Baitalami.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 17