Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 17:5-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Yana sa kwalkwali na tagulla a kansa, yana kuma saye da sulke na tagulla wanda nauyinsa ya fi shekel dubu biyar (5,000).

6. Ya sa safa ta tagulla a ƙafafunsa, yana kuma da mashi na tagulla saɓe a kafaɗarsa.

7. Gorar mashinsa ta yi kama da dirkar masaƙa. Nauyin ruwan mashinsa na baƙin ƙarfe shekel ɗari shida ne. Mai ɗaukar masa garkuwa yana tafe a gabansa.

8. Goliyat ya ta da murya da ƙarfi, ya yi kira ga rundunar Isra'ila, ya ce, “Don me kuka fito ku jā dāgar yaƙi? Ai, ni Bafiliste ne, ku kuwa barorin Saul! Ku zaɓi mutum guda daga cikinku ya gangaro nan wurina.

9. Idan ya iya yaƙi da ni, ya kashe ni, to sai mu zama bayinku, amma idan na fi ƙarfinsa, na kashe shi, sai ku zama bayinmu, ku bauta mana.”

10. Ya ƙara da cewa, “Na raina rundunan Isra'ila yau. Ku ba ni mutumin da zan yi yaƙi da shi.”

11. Sa'ad da Saul da dukan Isra'ilawa suka ji maganganun da Bafilisten nan yake faɗa, sai suka karaya, suka tsorata ƙwarai.

12. Dawuda kuwa ɗan Yesse ne, wanda yake mutumin Efrata, ta Baitalami cikin Yahuza, yana da 'ya'ya maza guda takwas, ya kuwa riga ya tsufa a zamanin Saul.

13. Manyan 'ya'yansa maza uku sun tafi yaƙi tare da Saul. Sunan babban ɗan, Eliyab, na biye da shi kuma, Abinadab, na ukun kuwa Shimeya.

14. Dawuda shi ne auta. Sa'ad da manyan 'yan'uwansa uku suka tafi tare da Saul wurin yaƙi,

15. Dawuda yakan koma Baitalami lokaci lokaci domin kiwon tumakin mahaifinsa.

16. Goliyat yana ta tsokanar Isra'ilawa safe da maraice, har kwana arba'in.

17. Wata rana ke nan, sai Yesse ya ce wa Dawuda, ɗansa, “Ka ɗauki wannan tumammen hatsi, da malmalar abinci goma, ka kai wa 'yan'uwanka da sauri a sansanin.

Karanta cikakken babi 1 Sam 17