Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 14:43-51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

43. Sa'an nan Saul ya ce wa Jonatan, “Ka faɗa mini abin da ka yi!” Jonatan ya ce masa, “Na ɗanɗana 'yar zuma ne da na lakata da kan sandan da yake hannuna, ga ni, a shirye nake in mutu.”

44. Sai Saul ya ce, “Allah ya yi mini abin da ya fi haka, idan ba a kashe ka ba, Jonatan.”

45. Amma jama'a suka ce wa Saul, “Jonatan da ya yiwo babbar nasara domin Isra'ila, a ce za a kashe shi? Kai, a'a! Mun yi alkawari ga Ubangiji mai rai, Jonatan ba zai yi hasarar ko gashi guda daga kansa ba. Abin da ya yi a yau, da taimakon Allah ne ya yi.” Da haka mutane suka ceci Jonatan, har ba a kashe shi ba.

46. Sa'an nan Saul ya komo daga runtumar Filistiyawa, suka koma yankin ƙasarsu.

47. Sa'ad da Saul ya ci sarautar Isra'ila, ya yi yaƙi da dukan abokan gābansa da suke kewaye da shi. Ya yi yaƙi da Mowabawa da Ammonawa, da Edomawa, da sarakunan Zoba, da Filistiyawa. Duk inda ya yi yaƙi ya sami nasara.

48. Ya yi aikin jaruntaka, ya bugi Amalekawa, ya ceci Isra'ilawa daga hannun dukan waɗanda suka taso musu.

49. 'Ya'yan Saul, maza ke nan, Jonatan, da Yishwi, da Malkishuwa. Yana kuma da 'ya'ya mata biyu, Merab, 'yar fari, da Mikal.

50. Sunan matarsa kuwa Ahinowam 'yar Ahimawaz. Sunan shugaban rundunansa kuwa Abner ne, ɗan Ner, kawunsa.

51. Kish mahaifin Saul, da Ner mahaifin Abner, 'ya'yan Abiyel ne.

Karanta cikakken babi 1 Sam 14