Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 14:31-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Filistiyawa sun sha ɗibga a wannan rana, tun daga Mikmash har zuwa Ayalon. Isra'ilawa suka tafke da yunwa.

32. Sai suka yi warwason ganima, suka kwashe tumaki, da shanu, da maruƙa, suka yanyanka su, suka ci naman ɗanye.

33. Sai aka faɗa wa Saul, “Ga shi, mutane suna yi wa Ubangiji laifi, suna cin nama ɗanye.”Saul kuwa ya ce, “Kun ci amana. Ku mirgino babban dutse a nan wurina.”

34. Sa'an nan ya ce, “Ku tafi ku faɗa wa jama'a duka, su kawo takarkarai da tumaki a nan, su yanyanka su, su ci a nan, don kada su yi wa Ubangiji zunubi da cin nama ɗanye.” Sai dukansu suka kawo takarkaransu a wannan dare, suka yanyanka a wurin.

35. Saul kuwa ya gina wa Ubangiji bagade. Shi ne bagade na farko da ya gina wa Ubangiji.

36. Sa'an nan Saul ya ce, “Mu tafi, mu fallasa Filistiyawa da dare har wayewar gari, kada ko mutum ɗaya daga cikinsu ya tsira.”Sai suka ce masa, “Ka yi abin da ka ga ya yi maka kyau.” Amma firist ɗin ya ce, “Bari mu yi tambaya ga Allah.”

37. Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, ya ce, “In runtumi Filistiyawa? Za ka bashe su ga Isra'ilawa?” Amma Ubangiji bai amsa masa a wannan rana ba.

38. Sai Saul ya ce wa shugabanni, “Ku zo nan dukanku don mu bincike, mu san zunubin da aka yi a yau.

39. Hakika, duk wanda ya yi laifin za a kashe shi, ko da Jonatan ne, ɗana.” Amma ba wanda ya ce kome.

40. Ya kuma ce, “Dukanku ku tsaya waje ɗaya, ni kuma da Jonatan, ɗana, mu tsaya waje ɗaya.”Sai jama'ar suka ce wa Saul, “Ka yi abin da ya yi maka kyau.”

41. Sa'an nan Saul ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, me ya sa ba ka amsa mini ba a wannan rana? Idan wannan laifina ne, ko kuwa na ɗana, Jonatan, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka nuna mana.” Sai amsa ta nuna Jonatan da Saul ne, jama'a kuwa suka kuɓuta.

42. Sa'an nan Saul ya ce, “A jefa kuri'a tsakanina da ɗana Jonatan.” Kuri'a kuwa ta fāɗa a kan Jonatan.

43. Sa'an nan Saul ya ce wa Jonatan, “Ka faɗa mini abin da ka yi!” Jonatan ya ce masa, “Na ɗanɗana 'yar zuma ne da na lakata da kan sandan da yake hannuna, ga ni, a shirye nake in mutu.”

44. Sai Saul ya ce, “Allah ya yi mini abin da ya fi haka, idan ba a kashe ka ba, Jonatan.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 14