Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 13:8-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ya dakata kwana bakwai bisa ga adadin lokacin da Sama'ila ya ɗibar masa, amma Sama'ila bai iso Gilgal ba. Mutane suka yi ta watsewa suna barin Saul.

9. Sai Saul ya ce, “Ku kawo mini hadaya ta ƙonawa da hadayun salama.” Ya kuwa miƙa hadaya ta ƙonawa.

10. Yana gama miƙa hadayar ke nan, sai ga Sama'ila ya iso.Saul kuwa ya fita don ya tarye shi, ya gaishe shi.

11. Sai Sama'ila ya ce, “Me ke nan ka yi?”Saul ya amsa ya ce, “Don na ga mutane suna watsewa, suna barina, kai kuma ba ka zo daidai lokacin ba, ga kuma Filistiyawa sun tattaru a Mikmash.

12. Sai na yi tunani cewa, ‘Yanzu Filistiyawa za su gangaro su fāɗa mini a Gilgal, ni kuwa ban riga na roƙi Ubangiji ba,’ don haka ya zama mini tilas in miƙa hadaya ta ƙonawa!”

13. Sama'ila kuwa ya ce wa Saul, “Ka yi wauta, ba ka kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba. Dā Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra'ila har abada.

14. Amma yanzu sarautarka ba za ta tabbata ba, gama Ubangiji ya riga ya sami mutum wanda yake so. Ubangiji ya riga ya naɗa shi ya zama sarkin jama'arsa, domin ba ka kiyaye umarnin Ubangiji ba.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 13