Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 10:21-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sai kuma ya sa kabilar Biliyaminu ta guso iyali iyali, kuri'a kuwa ta faɗa a kan iyalin Matri. Sa'an nan kuma ya guso da iyalin Matri mutum mutum, kuri'a ta faɗa a kan Saul, ɗan Kish. Amma sa'ad da suka neme shi, ba a same shi ba.

22. Suka yi tambaya a wurin Ubangiji, suka ce, “Ko akwai wani dabam?”Ubangiji ya ce, “Ai, ga shi can, ya ɓuya cikin kayayyaki.”

23. Sai suka sheƙa, suka fito da shi daga wurin da ya ɓuya, ya tsaya cikin mutane, ya fi kowa tsayi da misalin ƙafa guda.

24. Sama'ila ya ce wa dukan jama'a, “Kun gan shi? Shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa, babu wani kamarsa a cikin dukan jama'a.”Jama'a duka kuwa suka yi sowa suka ce, “Ran sarki ya daɗe!”

25. Sa'an nan Sama'ila ya faɗa wa jama'a ka'idodin sarautar. Ya rubuta su cikin littafi, ya ajiye a wuri mai tsarki. Sa'an nan ya sallami jama'a duka kowa ya koma gidansa.

26. Saul kuma ya koma gidansa a Gibeya tare da waɗansu jarumawa da Allah ya taɓa zuciyarsu.

27. Amma waɗansu shashashan mutane suka ce, “Ƙaƙa wannan yaro zai iya cetonmu?” Suka raina shi, ba su kawo masa gaisuwa ba. Amma bai ce kome ba.

Karanta cikakken babi 1 Sam 10