Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 1:4-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Duk lokacin da Elkana ya miƙa hadayarsa, sai ya ba Feninna da 'ya'yanta mata da maza nasu rabo.

5. Amma Hannatu, sai ya ba ta babban rabo guda ɗaya, gama yana ƙaunarta, amma Ubangiji ya kulle mahaifarta.

6. Kishiyarta takan tsokane ta don ta ji haushi, gama Ubangiji ya hana mata haihuwa.

7. Haka aka yi ta yi kowace shekara, duk lokacin da suka tafi domin yin sujada, sai Feninna ta tsokane ta. Don haka Hannatu ta yi ta kuka, ta ƙi cin abinci.

8. Elkana mijinta kuwa, ya ce mata, “Hannatu, me ya sa kike kuka? Me ya sa kike ƙin cin abinci? Me ya sa zuciyarki ta ɓaci? Ni ban fi 'ya'ya maza goma a gare ki ba?”

9. Wata rana a Shilo bayan da sun gama cin abinci, sai Hannatu ta tashi. Eli, firist, kuwa yana zaune a kujera a bakin ƙofar masujadar Ubangiji.

10. Hannatu tana fama da baƙin ciki ƙwarai, sai ta yi addu'a, tana kuka da ƙarfi ga Ubangiji.

11. Ta yi wa'adi, ta ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, idan lalle ka dube ni, ni baiwarka, ka tuna da ni, ba ka manta da ni baiwarka ba, amma ka ba ni ɗa, ni ma sai in ba da shi ga Ubangiji dukan kwanakinsa, aska kuwa ba za ta taɓa kansa ba.”

12. Eli kuwa ya lura da bakin Hannatu sa'ad da take yin addu'a.

13. Gama ta yi addu'ar a zuci, ba a jin muryarta, sai dai leɓun motsi. Don haka Eli ya zaci tana maye ne,

Karanta cikakken babi 1 Sam 1