Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 19:20-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Yahudawa da yawa kuwa sun karanta wannan sanarwa, domin wurin da aka gicciye Yesu kusa da birni ne. An kuwa rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da kuma Helenanci.

21. Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce wa Bilatus, “Kada ka rubuta ‘Sarkin Yahudawa’, sai dai ka rubuta, ‘A faɗarsa shi ne Sarkin Yahudawa.’ ”

22. Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta na rubuta ke nan.”

23. Bayan soja sun gicciye Yesu, suka ɗibi tufafinsa, suka kasa kashi huɗu, kowane soja ya ɗauki kashi guda. Suka kuma ɗauki taguwa tasa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta.

24. Sai suka ce wa juna, “Kada mu tsaga ta, sai dai mu yi kuri'a a kanta, mu ga wanda zai ci.” Wannan kuwa domin a cika Nassi ne cewa,“Sun raba tufafina a junansu.Taguwata kuwa suka jefa kuria akanta”

25. Haka fa sojan suka yi. To, kusa da gicciyen Yesu kuwa da uwa tasa, da 'yar'uwa tata, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya, suna tsaye.

26. Da Yesu ya ga uwa tasa, da almajirin nan da yake ƙauna suna tsaye kusa, ya ce wa uwa tasa, “Iya, ga ɗanki nan!”

27. Sa'an nan ya ce wa almajirin, “Ga tsohuwarka nan!” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.

28. Bayan haka, Yesu da ya san duk an gama kome, domin a cika Nassi sai ya ce, “Ina jin ƙishirwa.”

29. To, akwai wani gora cike da ruwan tsami a ajiye a nan. Sai suka jiƙa soso da ruwan tsamin, suka soka a sandan izob suka kai bakinsa.

30. Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin nan ya ce, “An gama!” Sa'an nan ya sunkuyar da kansa ya ba da ransa.

31. Da yake ran nan ranar shiri ce, don kada a bar jikuna a gicciye ran Asabar (domin wannan Asabar ɗin babbar rana ce), sai Yahudawa suka roƙi Bilatus a karya ƙafafunsu, a kuma ɗauke jikunan.

32. Sai soja suka zo suka karya ƙafafun na farkon nan, da kuma na ɗayan da aka gicciye tare da shi.

33. Amma da suka zo wurin Yesu, suka kuma ga ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba.

34. Sai dai ɗaya daga cikin sojan nan ya soke shi da mashi a kwiɓi, nan da nan sai ga jini da ruwa suka gudano.

35. Wanda ya gani ɗin kuwa shi ya ba da shaida kan haka, shaida tasa kuwa gaskiya ce, ya kuma san gaskiya yake faɗa, domin ku ma ku ba da gaskiya.

Karanta cikakken babi Yah 19