Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 18:10-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Bitrus kuwa da yake yana da takobi, ya zaro ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama. Sunan bawan Malkus.

11. Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Mai da takobinka kube. Ba sai in sha ƙoƙon da Uba ya ba ni in sha ba?”

12. Sai ƙungiyar soja da shugabansu, da dogaran nan na Yahudawa suka kama Yesu, suka ɗaure shi,

13. suka tafi da shi wurin Hanana da fari, don shi surukin Kayafa ne, wanda yake shi ne babban firist a shekaran nan.

14. Kayafa kuwa shi ne ya yi wa Yahudawa shawara, cewa ya fiye musu mutum ɗaya ya mutu saboda jama'a.

15. Sai Bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajiri. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har gidan firist ɗin tare da Yesu,

16. Bitrus kuwa ya tsaya a bakin ƙofa daga waje. Sai ɗaya almajirin da yake sananne ga babban firist ya fita, ya yi magana da wadda take jiran ƙofa, sa'an nan ya shigo da Bitrus.

17. Baranyar da yake jiran ƙofar kuwa ta ce wa Bitrus, “Anya! Kai ma ba cikin almajiran mutumin nan kake ba?” Ya ce, “A'a, ba na ciki.”

18. To, barori da dogaran Haikali kuwa sun hura wutar gawayi, don ana sanyi, suna tsaitsaye, suna jin wutar. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin wutar.

19. Sai babban firist ya tuhumi Yesu a kan almajiransa da kuma koyarwa tasa.

20. Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba.

21. Don me kake tuhumata? Tuhumi waɗanda suka saurare ni a kan abin da na faɗa musu, ai, sun san abin da na faɗa.”

22. Da ya faɗi haka, wani daga cikin dogaran da suke tsaye kusa, ya mari Yesu, ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?”

23. Yesu ya amsa masa ya ce, “In na faɗi mugun abu to, ka ba da shaida kan haka. In kuwa daidai na faɗa, to, don me za ka mare ni?”

24. Sai Hanana ya aika da shi a ɗaure wurin Kayafa, babban firist.

25. To, Bitrus kuwa yana tsaye yana jin wuta. Sai suka ce masa, “Anya! Kai ma ba cikin almajiransa kake ba?” Sai ya mūsu ya ce, “A'a, ba na ciki.”

Karanta cikakken babi Yah 18