Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 12:15-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. “Kada ki ji tsoro, ya ke 'yar Sihiyona,Ga sarkinki na zuwa a kan aholakin jaki!”

16. Da fari almajiransa ba su gane abin nan ba, amma bayan an ɗaukaka Yesu, suka tuna abin nan a rubuce yake game da shi, har ma aka yi masa shi.

17. Taron da yake tare da shi sa'ad da ya kira Li'azaru yă fito daga kabari, ya tashe shi daga matattu, su suka riƙa shaidarwa da haka.

18. Shi ya sa taron suka fita taryensa, don sun ji ya yi mu'ujizan nan.

19. Sai Farisiyawa suka ce wa juna, “Kun ga! Ba abin da muka iya! Ai, duk duniya tana bayansa.”

20. To, a cikin waɗanda suka zo idin yin sujada akwai waɗansu Helenawa.

21. Sai suka zo wurin Filibus, mutumin Betsaida ta ƙasar Galili, suka roƙe shi suka ce, “Maigida, muna bukatar mu gana da Yesu.”

22. Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawas, Andarawas kuma ya zo da Filibus, suka gaya wa Yesu.

23. Yesu ya amsa musu ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum.

24. Lalle hakika, ina gaya muku, in ba an binne ƙwayar alkama ta mutu ba, za ta zauna ita kaɗai. Amma in ta mutu sai ta hayayyafa.

25. Mai ƙaunar ransa zai rasa shi. Wanda kuwa ya ƙi ransa a duniyan nan, ya kiyaye shi ke nan, har ya zuwa rai madawwami.

26. Wanda duk zai bauta mini, ya bi ni. Inda nake kuma, nan bawana zai kasance shi ma. Kowa yake bauta mini, Uba zai girmama shi.”

27. “Yanzu ina jin nauyi a raina. Me zan ce kuwa? In ce, ‘Ya Uba ka ɗauke mini wannan lokaci’? A'a, ai, dā ma na zo ne takanas domin wannan lokaci.

28. Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi,”

29. Da taron da yake tsaye a wurin suka ji muryar, suka ce, “An yi cida.” Waɗansu kuwa suka ce, “Wani mala'ika ne ya yi masa magana.”

30. Yesu ya amsa ya ce, “Ba saboda ni aka yi wannan muryan nan ba, sai dominku.

Karanta cikakken babi Yah 12