Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 4:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan wannan na duba, sai ga wata ƙofa a buɗe a Sama. Muryar farko da na ji dā, mai kama da ƙaho, ta ce mini, “Hawo nan, zan nuna maka abin da lalle ne ya auku bayan wannan.”

2. Nan da nan kuwa Ruhu ya iza ni, sai ga wani kursiyi a girke a Sama, da wani a zaune a kai.

3. Na zaunen kuwa ya yi kama da yasfa da yakutu. Kewaye da kursiyin kuma akwai wani bakan gizo mai kama da zumurrudu.

4. Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyai ashirin da huɗu, da dattawa ashirin da huɗu a zaune a kai, masu fararen tufafi, da kuma kambin zinariya a kansu.

5. Sai walƙiya take ta fitowa daga kursiyin, da ƙararraki, da kuma aradu. A gaban kursiyin kuma fitilu bakwai suna ci, waɗanda suke Ruhohin nan na Allah guda bakwai.

Karanta cikakken babi W. Yah 4