Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 22:8-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ni Yahaya, ni ne na ji, na kuma ga waɗannan abubuwa. Sa'ad da kuwa na ji su, na kuma gan su, sai na fāɗi a gaban mala'ikan da ya nuna mini su, domin in yi masa sujada.

9. Amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye maganar littafin nan. Allah za ka yi wa sujada.”

10. Ya kuma ce mini, “Kada ka rufe maganar annabcin littafin nan, domin lokaci ya kusa.

11. Marar gaskiya yă yi ta rashin gaskiyarsa, fajiri kuwa yă yi ta fajircinsa, adali kuwa yă yi ta aikata adalcinsa, wanda yake tsattsarka kuwa ya yi ta zamansa na tsarki.”

12. “Ga shi, ina zuwa da wuri, tare da sakamakon da zan yi wa kowa gwargwadon abin da ya yi.

13. Ni ne Alfa, Ni ne Omega, Ni ne na Farko, Ni ne na Ƙarshe.”

14. Albarka tā tabbata ga masu wanke rigunansu, domin su sami izinin ɗiba daga itacen rai, su kuma shiga birnin ta ƙofa.

15. Waɗanda aka hana shiga birnin kuwa, su ne fajirai, da masu sihiri, da fasikai, da masu kisankai, da masu bautar gumaka, da kuma duk wanda yake son ƙarya, yake kuma yinta.

16. “Ni Yesu, na aiko mala'ikana a gare ka, da wannan shaida saboda ikilisiyoyi. Ni ne tsatson Dawuda, da zuriyarsa, Gamzaki mai haske.”

17. Ruhu da amarya suna cewa, “Zo.” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta.

18. Ina yi wa duk mai jin maganar annabcin littafin nan kashedi, in wani ya yi wani ƙari a kanta, Allah zai ƙara masa bala'in da aka rubuta a littafin nan.

19. In kuma wani ya yi ragi a maganar littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai, da na tsattsarkan birnin, waɗanda aka rubuta a littafin nan.

Karanta cikakken babi W. Yah 22