Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 22:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sai ya ce mini, “Wannan magana tabbatacciya ce, ta gaskiya ce kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa ya aiko mala'ikansa, ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba.”

7. “Ga shi kuwa, ina zuwa da wuri. Albarka tā tabbata ga wanda yake kiyaye maganar annabcin littafin nan.”

8. Ni Yahaya, ni ne na ji, na kuma ga waɗannan abubuwa. Sa'ad da kuwa na ji su, na kuma gan su, sai na fāɗi a gaban mala'ikan da ya nuna mini su, domin in yi masa sujada.

9. Amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye maganar littafin nan. Allah za ka yi wa sujada.”

10. Ya kuma ce mini, “Kada ka rufe maganar annabcin littafin nan, domin lokaci ya kusa.

11. Marar gaskiya yă yi ta rashin gaskiyarsa, fajiri kuwa yă yi ta fajircinsa, adali kuwa yă yi ta aikata adalcinsa, wanda yake tsattsarka kuwa ya yi ta zamansa na tsarki.”

12. “Ga shi, ina zuwa da wuri, tare da sakamakon da zan yi wa kowa gwargwadon abin da ya yi.

Karanta cikakken babi W. Yah 22