Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 21:2-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sai na ga tsattsarkan birni kuma, Sabuwar Urushalima, tana saukowa daga Sama daga wurin Allah, shiryayyiya kamar amaryar da ta yi ado saboda mijinta.

3. Na kuma ji wata murya mai ƙara daga kursiyin, tana cewa, “Kun ga, mazaunin Allah na tare da mutane. Zai zauna tare da su, za su zama jama'arsa, Allah kuma shi kansa zai kasance tare da su,

4. zai share musu dukkan hawaye. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba, don abubuwan dā sun wuce.”

5. Sai na zaune a kan kursiyin ya ce, “Kun ga, ina yin kome sabo.” Ya kuma ce, “Rubuta wannan, domin maganar nan tabbatacciya ce, gaskiya ce kuma.”

6. Sai ya ce mini, “An gama! Ni ne Alfa, Ni ne Omega, Ni ne na Farko, Ni ne kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi ruwa daga maɓuɓɓugar ruwan rai kyauta.

7. Duk wanda ya ci nasara, zai ci wannan gādo, wato, in zama Allahnsa, shi kuma ya zama ɗa a gare ni.

8. Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”

9. Sai kuma ɗaya daga cikin mala'ikun nan bakwai, masu tasoshin nan bakwai, cike da bala'i bakwai na ƙarshe, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka amarya, matar Ɗan Ragon.”

10. Sai ya ɗauke ni, Ruhu yana iza ni, ya kai ni wani babban dutse mai tsawo, ya nuna mini tsattsarkan birnin Urushalima yana saukowa daga Sama daga wurin Allah,

11. yana tare da ɗaukakar Allah. Hasken birnin yana ƙyalƙyali kamar wani irin nadirin dutse mai daraja, kamar yasfa, garau kamar ƙarau.

12. Yana da babban garu mai tsawo, da ƙofar gari goma sha biyu, a ƙofofi ɗin da akwai mala'iku goma sha biyu. A jikin ƙofofin kuma an rubuta sunayen kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila,

13. a gabas, ƙofa uku, a yamma ƙofa uku, a kudu ƙofa uku, a arewa kuma ƙofa uku.

14. Garun birnin kuwa, tana da dutsen harsashi goma sha biyu, a jikinsu kuma an rubuta sunayen manzannin nan goma sha biyu na Ɗan Ragon.

15. Shi wanda ya yi mini magana kuwa yana da sandar awo ta zinariya, domin ya auna birnin, da ƙofofinsa, da garunsa.

16. Birnin murabba'i ne, tsawonsa da fāɗinsa duka ɗaya ne. Sai ya auna birnin da sandarsa, mil dubu da ɗari biyar, tsawonsa, da fāɗinsa da zacinsa, duka ɗaya suke.

17. Ya kuma auna garunsa, kamu ɗari da arba'in da huɗu ne na mutum, wato, na mala'ika ke nan.

Karanta cikakken babi W. Yah 21