Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 19:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Rundunonin Sama, saye da lallausan lilin fari mai tsabta, suna a biye da shi a kan fararen dawakai.

15. Daga cikin bakinsa wani kakkaifan takobi yake fitowa, wanda zai sare al'ummai da shi, zai kuwa mallake su da tsanani ƙwarai, zai tattake mamatsar inabi, ta tsananin fushin Allah Maɗaukaki.

16. Da wani suna a rubuce a jikin rigarsa, har daidai cinyarsa, wato Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.

17. Sa'an nan na ga wani mala'ika tsaye a jikin rana. Sai kuma ya kira dukkan tsuntsaye da suke tashi a sararin sama, da murya mai ƙarfi, ya ce, “Ku zo, ku taru wurin babban bikin nan na Allah,

18. ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaƙi, da naman ƙarfafa, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman kowa da kowa, wato, na ɗa da na bawa, na yaro da na babba.”

19. Sai na ga dabbar nan, da sarakunan duniya, da rundunoninsu, sun taru, don su yaƙi wanda yake kan dokin, da kuma rundunarsa.

20. Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.

Karanta cikakken babi W. Yah 19