Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 1:6-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. ya mai da mu firistoci, mallakar Allah Ubansa. Amin.

7. Ga shi, zai zo a cikin gajimare, kowa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka a kansa. Wannan haka yake. Amin.

8. “Ni ne Alfa. Ni ne Omega,” in ji Ubangiji Allah, wanda yake a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma a nan gaba, Maɗaukaki.

9. Ni ne Yahaya, ɗan'uwanku abokin tarayyarku a cikin tsanani, da mulki, da jimiri da suke a cikin Yesu. Ina a can tsibirin da ake kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu.

10. A ranar Ubangiji ya zamana Ruhu ya iza ni, sai na ji wata murya mai ƙara a bayana kamar ta ƙaho,

11. tana cewa, “Rubuta abin da ka gani a littafi, ka aika wa ikilisiyoyin nan bakwai, wato ta Afisa, da ta Simirna, da ta Birgamas, da ta Tayatira, da ta Sardisu, da ta Filadalfiya, da kuma ta Lawudikiya.”

12. Sai na juya in ga wanda yake yi mini magana, da juyawata kuwa, sai na ga fitilu bakwai na zinariya.

13. A tsakiyar fitilun nan kuwa, na ga wani kamar Ɗan Mutum, saye da riga har idon sawu, ƙirjinsa kuma da ɗamarar zinariya.

14. Kansa da gashinsa farare fat ne kamar farin ulu, farare fat kamar alli, idanunsa kamar harshen wuta,

15. ƙafafunsa kamar gogaggiyar tagulla, kamar wadda aka tace a maƙera, muryarsa kuma kamar ƙugin ruwaye masu gudu.

16. Yana riƙe da tauraro bakwai a hannunsa na dama, daga bakinsa kuma takobi mai kaifi biyu yake fitowa. Fuskarsa tana haske kamar rana a tsaka.

17. Da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa kamar na mutu. Amma ya ɗora mini hannunsa na dama, ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne na Farko. Ni ne na Ƙarshe,

18. ni ne kuma Rayayye. Dā na mutu, amma ga shi a yanzu, ina a raye har abada abadin, ina kuwa da mabuɗan mutuwa da na Hades.

Karanta cikakken babi W. Yah 1