Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 4:11-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Kaciyar da aka yi masa alama ce, wato tabbatacciyar shaida ce ta samun adalci, albarkacin bangaskiyar da yake da ita tun ba a yi masa kaciya ba. Wannan kuwa, domin yă zama uban dukkan masu ba da gaskiya ne, domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba,

12. haka kuma yă zama uban masu kaciya, waɗanda ba kaciya kaɗai suke da ita ba, har ma suna bin hanyar bangaskiyar nan ta kakanmu Ibrahim, wadda shi ma ya bi, tun ba a yi masa kaciya ba.

13. Alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa, cewa zai zama magājin duniya, ba ta Shari'a aka yi masa ba, amma domin ya ba da gaskiya ne, shi ya sa Allah ya karɓe shi mai adalci ne.

14. In dai masu bin Shari'a su ne magāda, ashe, bangaskiya ta zama banza ke nan, alkawarin nan kuma ya wofinta,

15. don Shari'a tana jawo fushin Allah. A inda ba Shari'a kuwa, ba keta umarni ke nan.

16. Saboda haka al'amarin ya dogara ga bangaskiya, domin yă zama bisa ga alheri, don kuma a tabbatar da alkawarin nan ga dukkan zuriyar Ibrahim, ba ga masu bin Shari'a kaɗai a cikinsu ba, har ma ga waɗanda suke da bangaskiya irin Ibrahim, shi da yake ubanmu duka.

Karanta cikakken babi Rom 4