Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 3:21-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. A yanzu, ba kuwa a game da shari'a ba, an bayyana wata hanyar samun adalcin Allah, wadda ma Attaura da littattafan annabawa suke yi wa shaida.

22. Adalcin nan na Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya ga Yesu Almasihu, na masu ba da gaskiya ne dukka, ba kuwa wani bambamci,

23. gama 'yan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah.

24. Amma ta wurin alherin da Allah ya yi musu kyauta, sun sami kuɓuta ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi.

25. Allah kuwa ya ayyana Yesu Almasihu ya zama hadayar sulhu, ta wurin ba da gaskiya ga jininsa. Allah kuwa ya yi haka domin yă nuna adalcinsa ne, domin dā saboda haƙurinsa ya jingine zunuban da aka gabatar,

26. domin a nuna adalcinsa a wannan zamani, wato a bayyana shi kansa mai adalci ne, mai kuɓutar da duk mai gaskatawa da Yesu kuma.

27. To, ina kuma fariyarmu ta shiga? Ina kuwa! Ta wace hanya aka kawar da ita? Ta aikin lada? A'a, sai dai ta hanyar bangaskiya.

28. Domin mun amince, cewa ta bangaskiya ne mutum yake kuɓuta, ba ta kiyaye ayyukan Shari'a ba.

29. Wato Allah, Allahn Yahudawa ne kurum? Ashe, ba na al'ummai ba ne kuma? Hakika na al'ummai ne ma,

30. tun da yake Allah ɗaya ne, zai kuwa kuɓutar da masu kaciya ta wurin bangaskiya, marasa kaciya ma ta wannan bangaskiya.

31. Wato mun soke Shari'a ke nan ta bangaskiyar nan? A'a, ko kusa! Sai tabbatar da ita muka yi.

Karanta cikakken babi Rom 3