Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 2:16-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. A wannan rana Allah zai yi wa 'yan adam shari'a a kan asiransu, ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga bishara da nake wa'azinta.

17. To, in ka ce kai Bayahude ne, cewa ka dogara da Shari'a, har kana taƙama da Allah,

18. ka san abin da yake so, da yake kuma ka karantu da Shari'a, ka iya bambancewa da abubuwa mafifita,

19. har ka amince kai kanka jagoran makafi ne, haske ga waɗanda suke a cikin duhu,

20. mai horon marasa azanci, mai koya wa sababbin shiga, don a cikin Shari'ar kana da ainihin sani da ainihin gaskiya,

21. to, kai mai koya wa wani, ba ka koya wa kanka? Kai mai wa'azin kada a yi sata, shin, kai ba ka yi ne?

22. Kai mai cewa kada a yi zina, kai ba ka yi ne? Kai mai ƙyamar gumaka, ba ka sata a ɗakin gunki ne?

23. Kai mai taƙama da Shari'a, ashe, ba wulakanta Allah kake yi ba ta keta Shari'ar?

24. Yadda yake a rubuce cewa, “A sanadinku ne al'ummai suke saɓon sunan Allah.”

25. Lalle yin kaciya yana da amfani, in dai kana bin Shari'ar. Amma in kai mai keta shari'ar ne, kaciyarka ba a bakin kome take ba.

26. In kuwa marar kaciya yana kiyaye farillan Shari'a, ashe, ba sai a lasafta rashin kaciyarsa a kan kaciya ba?

27. Ashe, wanda rashin kaciya al'adarsa ce, ga shi kuwa, yana bin Shari'ar daidai, ba sai yă kāshe ka ba, kai da kake da Shari'a a rubuce da kuma kaciya, amma kana keta Shari'ar?

28. Gama Bayahude na ainihi ba mutum ne wanda yake Bayahude bisa siffar jikinsa na fili ba, kaciya ta ainihi kuwa ba kaciya ce ta fili ta fatar jiki ba.

29. Wanda yake Bayahude a zuci, ai, shi ne Bayahude. Kaciyar ainihi kuwa a zuci take, wato ta ruhu, ba ta zahiri ba. Irin wannan mutum, Allah ne yake yaba masa, ba ɗan adam ba.

Karanta cikakken babi Rom 2