Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 1:21-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Domin kuwa ko da yake sun san da Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi a kan shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyarsu marar fahimta kuma ta duhunta.

22. Suna da'awa cewa, su masu hikima ne, sai suka zama wawaye.

23. Sun sauya ɗaukakar Allah marar mutuwa da misalin siffar mutum mai mutuwa, da ta tsuntsaye, da ta dabbobi, da kuma ta masu jan ciki.

24. Saboda haka Allah ya sallama su ga rashin tsarkaka ta mugayen sha'awace-sha'awacensu, har su wulakanta jikinsu a junansu,

25. saboda sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, har yi wa halitta ibada, sun kuma bauta mata, sun ƙi su yi wa Mahalicci, shi wanda yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin.

26. Don haka Allah ya sallama su ga mugayen sha'awace-sha'awace masu banƙyama, har matansu suka sauya ɗabi'arsu ta halal, da wadda take ta haram.

27. Haka kuma maza suka bar ma'amalarsu ta halal da mata, jarabar juna ta ɗebe su, maza da maza suna aikata rashin kunya, suna jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.

28. Tun da yake sun ƙi su yarda su san Allah, Allah ya sallama su ga halin banza, su aikata abin kunya.

29. Su masu aikata rashin adalci ne ƙwarai, da mugunta, da kwaɗayi, da ƙeta. Masu hassada ne, da kisankai, da jayayya, da ha'inci, da kuma nukura gaya matuƙa. Macizan ƙaiƙayi ne,

30. da masu yanke, da maƙiyan Allah, da masu cin mutunci, da masu girmankai, da masu ruba, da masu haddasa mugunta, da marasa bin iyaye,

31. da marasa fahimta, da masu ta da alkawari, da marasa ƙauna, da marasa tausayi.

32. Waɗannan kuwa ko da yake sun san shari'ar Allah cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, sun cancanci mutuwa, duk da haka, ba aikata su kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon masu yinsu.

Karanta cikakken babi Rom 1