Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 3:10-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Koyanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin bishiya. Saboda haka duk bishiyar da bata bada 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.

11. “Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.

12. Ƙwaryar shiƙarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun, sai ya ƙone a wutar marar kasuwa.”

13. A lokacin nan ne Yesu ya zo daga ƙasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma.

14. Yahaya kuwa ya so ya hana shi, ya ce, “Ni da nake bukatar kai ka yi mini baftisma, ka zo gare ni?”

15. Amma Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin haka ne ya dace mu cika dukan adalci.” Sa'an nan Yahaya ya yardar masa.

Karanta cikakken babi Mat 3