Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 27:42-54 Littafi Mai Tsarki (HAU)

42. “Ya ceci waɗansu, ya kuwa kasa ceton kansa. Ai, Sarkin Isra'ila ne, yă sauko mana daga gicciyen yanzu, mu kuwa mā gaskata da shi.

43. Yā dogara ga Allah, to, Allah ya cece shi mana yanzu, in dai yana sonsa, don ya ce wai shi Ɗan Allah ne.”

44. Har 'yan fashin nan da aka gicciye su tare ma, su suka zazzage shi kamar waɗancan.

45. To, tun daga tsakar rana, duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.

46. Wajen ƙarfe uku kuma sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāni?” Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”

47. Da waɗansu na tsaitsayen suka ji haka, sai suka ce, “Mutumin nan na kiran Iliya ne.”

48. Sai nan da nan ɗaya daga cikinsu ya yiwo gudu, ya ɗauko soso ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha.

49. Amma sauran suka ce, “Ku bari mu gani ko Iliya zai zo ya ceci shi.”

50. Sai Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sa'an nan ya săki ransa.

51. Sai labulen da yake cikin Haikalin ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta yi girgiza, duwatsu kuma suka tsattsage.

52. Aka bubbuɗe kaburbura, tsarkaka da yawa da suke barci kuma suka tashi.

53. Suka firfito daga kaburburan, bayan ya tashi daga matattu, sai suka shiga tsattsarkan birnin, suka bayyana ga mutane da yawa.

54. Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”

Karanta cikakken babi Mat 27