Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 25:14-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. “Kamar mutum ne da zai yi tafiya, ya kira bayinsa, ya danƙa musu dukiyarsa.

15. Ya ba ɗaya talanti biyar, ɗaya talanti biyu, wani kuma ya ba shi ɗaya, kowa dai gwargwadon ƙarfinsa. Sa'an nan ya tafi.

16. Shi wanda ya karɓi talanti biyar ɗin nan, nan da nan sai ya je ya yi ta jujjuya su, har wuri ya bugi wuri.

17. Haka kuma wanda ya karɓi talanti biyu, shi ma sai wuri ya bugi wuri.

18. Amma wannan da ya karɓi talanti ɗaya ɗin, sai ya je ya tona rami ya ɓoye kuɗin ubangijinsa.

19. To, da aka daɗe sai ubangijin bayin nan ya dawo ya daidaita lissafi da su.

20. Shi wannan da ya karɓi talanti biyar sai ya matso ya kawo waɗansu talanti biyar, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyar, ga shi kuma, na ci ribar biyar.’

21. Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.’

22. Sai mai talanti biyun nan kuma ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyu, ga shi kuma, na ci ribar biyu.’

23. Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangijinka.’

24. Shi kuma wanda ya karɓi talanti guda ɗin, sai ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, na sani kai mutum ne mai tsanani, kana son girbi inda ba kai ka shuka ba, mai son banza ne.

25. Shi ya sa na ji tsoro, har na je na yi tono na ɓoye talantinka. To, ga kayanka nan!’

26. Sai ubangijinsa ya amsa masa ya ce, ‘Kai mugun bawa, malalaci! Ashe, ka sani ina girbi inda ba ni na shuka ba, ni kuma mai son banza ne?

27. Ya kamata ka sa kuɗina a ma'aji, da na dawo kuma da sai in karɓi abina har da riba!

28. Don haka sai ku karɓe talantin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan.

Karanta cikakken babi Mat 25