Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 23:25-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike suke da zalunci da zari.

26. Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.

27. “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar ƙasa kuke, masu kyan gani daga waje, daga ciki kuwa sai ƙasusuwan matattu da ƙazanta iri iri.

28. Haka nan a idon mutane ku adalai ne, amma ciki sai munafunci da mugun aiki.

29. “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi gini a kan kaburburan annabawa, kuna ƙawata gubbobin adalai.

30. Kuna cewa, ‘Da mun zauna a zamanin kakanninmu, da ba mu taya su zub da jinin annabawa ba.’

31. Ta haka kuka shaidi kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa.

32. To, sai ku cikasa ayyukan kakanninku!

33. Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta?

34. Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami'unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba.

35. Don alhakin jinin dukan adalai da aka zubar a duniya yă komo a kanku, tun daga jinin Habila adali, har ya zuwa na Zakariya ɗan Berikiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikalin da bagaden hadaya.

36. Hakika, ina gaya muku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani.”

37. “Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi!

38. Ga shi, an bar muku gidanku a yashe!

Karanta cikakken babi Mat 23