Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 17:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan kwana shida sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da ɗan'uwansa Yahaya, ya kai su a kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai.

2. Sai kamanninsa suka sāke a gabansu, fuskarsa ta yi annuri kamar hasken rana, tufafinsa kuma suka yi fari fat suna haske.

3. Ga shi, Musa da Iliya sun bayyana a gare su, suna magana da Yesu.

4. Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da muke nan wurin. In kana so, sai in kafa bukkoki uku a nan, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.”

5. Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”

6. Da almajiran suka ji haka, sai suka faɗi ƙasa, tsoro ya kama su.

7. Sai Yesu ya zo ya taɓa su, ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”

8. Da suka ɗaga kai ba su ga kowa ba, sai Yesu kaɗai.

9. Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”

10. Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, yaya malaman Attaura suke cewa, lalle ne Iliya ya riga zuwa?”

11. Ya amsa ya ce, “Lalle Iliya zai zo ne, zai kuwa raya dukan abubuwa.

12. Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa san shi ne ba, har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka kuma Ɗan Mutum zai sha wuya a hannunsu.”

13. Sa'an nan ne almajiran suka gane, ashe, zancen Yahaya Maibaftisma yake yi musu.

14. Da suka isa wurin taro, sai wani mutum ya zo gare shi, ya durƙusa a gabansa, ya ce,

15. “Ya Ubangiji, ka ji tausayin ɗana, yana farfaɗiya, yana shan wuya ƙwarai, sau da yawa yakan faɗa wuta da kuma ruwa.

16. Na kuwa kai shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”

Karanta cikakken babi Mat 17