Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 12:18-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. “Ga barana wanda na zaɓa!Ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai.Zan sa masa Ruhuna, zai kuma sanar da al'ummai hanyar gaskiya.

19. Ba zai yi husuma ko magana sama sama ba,Ba kuma wanda zai ji muryarsa tasa a titi.

20. Kyauron da ya tanƙwasa ba zai kakkarye shi ba,Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba,Har ya sa gaskiya ta ci nasara.

21. Al'ummai kuma za su sa zuciya ga sunansa.”

22. Sai aka kawo masa wani beben makaho mai aljan, ya kuwa warkar da shi, har beben ya yi magana, ya kuma gani.

23. Mutane duk suka yi al'ajabi, suka ce, “Shin, ko wannan shi ne Ɗan Dawuda?”

24. Amma da Farisiyawa suka ji haka sai suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu kawai, wannan yake fitar da aljannu.”

25. Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Ba kuma gari ko gidan da ya rabu a kan gāba, yă ɗore.

26. In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, yā rabu a kan gāba ke nan. To, ta yaya mulkinsa zai ɗore?

27. In kuwa da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu, to, 'ya'yanku fa, da ikon wa suke fitarwa? Saboda haka su ne za su zama alƙalanku.

28. Ni kuwa in da ikon Ruhun Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan.

29. Yaya za a iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum a washe kayansa, in ba an fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin ba? Sa'an nan ne za a iya washe gidansa.

30. Wanda ba nawa ba ne, gāba yake da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.

31. “Don haka ina gaya muku, ā gafarta wa mutane kowane zunubi da saɓo, amma wanda ya saɓi Ruhun, ba za a gafarta masa ba.

32. Kowa ya aibata Ɗan Mutum, ā gafarta masa. Amma wanda ya aibata Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, duniya da lahira.”

33. “Ko dai ku ce itace kyakkyawa ne, 'ya'yansa kuma kyawawa, ko kuwa ku ce itace mummuna ne, 'ya'yansa kuma munana. Don itace, da 'ya'yansa ake gane shi.

34. Ku macizai! Yaya za ku iya yin maganar kirki, alhali kuwa ku mugaye ne? Don abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.

35. Mutumin kirki kam, ta kyakkyawar taskar zuciya tasa yakan yi abin kirki, mugu kuwa, ta mummunar taskar zuciya tasa yakan yi mugun abu.

36. Ina dai gaya muku, a Ranar Shari'a duk hululun da mutum ya yi, za a bincike shi.

37. Maganarka ce za ta kuɓutar da kai, ko kuma ta hukunta ka.”

38. Waɗansu malaman Attaura da Farisiyawa suka amsa masa suka ce, “Malam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.”

Karanta cikakken babi Mat 12