Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 9:21-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Yesu ya tambayi uban yaron, “Tun yaushe wannan abu ya same shi?” Uban ya ce, “Tun yana ƙarami.

22. Ya kuwa sha jefa shi a wuta da ruwa, don ya hallaka shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.”

23. Sai Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai, dukkan abu mai yiwuwa ne ga mai ba da gaskiya.”

24. Nan da nan sai uban yaron ya ɗaga murya ya ce, “Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata!”

25. Da Yesu ya ga taro na ɗungumowa a guje, sai ya tsawata wa baƙin aljanin ya ce masa, “Kai, beben aljan, na umarce ka ka rabu da shi, kada kuma ka ƙara hawansa.”

26. Bayan aljanin nan ya yi ihu, sai ya buge shi da gaske, jikinsa na rawa, ya rabu da shi. Yaron kuma ya zama kamar matacce, har ma yawancin mutane suka ce, “Ai, ya mutu!”

27. Amma Yesu ya kama hannunsa ya tashe shi, ya kuwa tashi tsaye.

28. Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a keɓe suka ce, “Me ya sa mu muka kasa fitar da shi?”

29. Sai ya ce musu, “Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a.”

30. Sai suka tashi daga nan, suka ratsa ƙasar Galili, bai kuwa so kowa ya sani ba,

31. domin yana koya wa almajiransa ne, yana ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane, za su kuwa kashe shi, sa'ad da aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.”

Karanta cikakken babi Mar 9