Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 9:38-52 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Sai ga wani daga cikin taron ya yi kira, ya ce, “Malam, ina roƙonka ka dubi ɗana da idon rahama, shi ne ke nan gare ni.

39. Ga shi, aljani yakan hau shi, yakan yi ihu ba zato ba tsammani. Aljanin yakan buge shi, jikinsa yana rawa, har bakinsa yana kumfa. Ba ya barinsa sai ya kukkuje shi ƙwarai.

40. Na kuwa roƙi almajiranka su fitar da shi, amma sun kasa.”

41. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku tsara marasa bangaskiya, kangararru! Har yaushe zan zama da ku, ina jure muku? Kawo ɗa naka nan.”

42. Yana zuwa, sai aljanin ya buge shi ƙwarai, jikinsa na rawa. Amma Yesu ya tsawata wa baƙin aljanin, ya warkar da yaron, ya kuma mayar wa ubansa da shi.

43. Duk aka yi mamakin girman ikon Allah.Tun dukansu suna mamakin duk abubuwan da yake yi, sai ya ce wa almajiransa,

44. “Maganar nan fa tă shiga kunnenku! Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane.”

45. Amma ba su fahimci maganan nan ba, an kuwa ɓoye musu ita ne don kada su gane. Su kuwa suna tsoron tambayarsa wannan magana.

46. Sai musu ya tashi a tsakaninsu a kan ko wane ne babbansu.

47. Amma da Yesu ya gane tunanin zuciyarsu, ya kama hannun wani ƙaramin yaro ya ajiye shi kusa da shi.

48. Ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi ƙanƙane yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuwa ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ke nan. Ai, wanda yake ƙarami a cikinku shi ne babba.”

49. Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Maigida, mun ga wani yana fitar da aljannu da sunanka, mun kuwa hana shi, domin ba ya binmu.”

50. Amma Yesu ya ce masa, “Kada ku hana shi. Ai, duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”

51. Da lokacin karɓarsa a Sama ya gabato, ya himmantu sosai ga zuwa Urushalima.

52. Sai ya aiki jakadu su riga shi gaba, suka kuwa tafi suka shiga wani ƙauyen Samariyawa su shisshirya masa.

Karanta cikakken babi Luk 9