Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 8:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ba da daɗewa ba Yesu ya zazzaga birni da ƙauye yana wa'azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa suna tare da shi,

2. da waɗansu mata da aka raba da baƙaƙen aljannu da kuma rashin lafiyarsu. Cikinsu da Maryamu mai suna Magadaliya, wadda aka fitar wa da aljannu bakwai,

3. da Yuwana matar Kuza, wakilin Hirudus, da Suzanatu, da kuma waɗansu da yawa da suka yi musu ɗawainiya da kayansu.

4. Da jama'a masu yawa suka taru, mutane suna ta zuwa gare shi gari da gari, sai ya yi musu misali ya ce.

5. “Wani mai shuka ya tafi shuka. Yana cikin yafa iri sai waɗansu suka fāɗi a hanya, aka tattake su, tsuntsaye suka tsince su.

6. Waɗansu kuma suka fāɗi a dutse. Da suka tsiro sai suka bushe, don ba danshi.

7. Waɗansu kuma suka fāɗi cikin ƙaya, suka tashi tare, har ƙayar ta sarƙe su.

8. Waɗansu kuwa suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka girma, suka yi ƙwaya riɓi ɗari ɗari.” Da ya faɗi haka, sai ya ta da murya ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

9. Almajiransa suka tambaye shi ma'anar misalin.

10. Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.

11. “To, misalin shi ne, irin Maganar Allah ne.

12. Waɗanda suka fāɗi a hanya su ne kwatancin waɗanda suka ji Maganar Allah, sa'an nan Iblis ya zo ya ɗauke Maganar daga zuciyarsu, don kada su ba da gaskiya su sami ceto.

13. Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya 'yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe.

14. Waɗanda suka fāɗi cikin ƙaya kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, amma a kwana a tashi, sai yawan taraddadin duniya, da dukiya, da shagalin duniya su sarƙe su, har su kasa yin amfani.

15. Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, suka riƙe ta kamkam da zuciya ɗaya kyakkyawa, suka jure har suka yi amfani.

Karanta cikakken babi Luk 8