Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 7:8-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.”

9. Da Yesu ya ji haka, ya yi mamakinsa, ya kuma juya ya ce wa taron da suke biye da shi, “Ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.”

10. Da waɗanda aka aika suka koma gidan, suka sami bawan garau.

11. Ba da daɗewa ba, Yesu ya tafi wani gari, wai shi Nayin, almajiransa da kuma babban taro suka tafi da shi.

12. Ya kusaci ƙofar garin ke nan, sai ga wani mamaci ana ɗauke da shi, shi kaɗai ne wajen uwa tasa, mijinta kuwa ya mutu. Mutanen gari da yawa sun rako ta.

13. Da Ubangiji ya gan ta, ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, “Daina kuka.”

14. Sa'an nan ya matso, ya taɓa makarar, masu ɗauka kuma suka tsaya cik. Sai Yesu ya ce, “Samari, na ce maka ka tashi.”

15. Mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuwa ya ba da shi ga uwa tasa.

16. Sai tsoro ya kama su duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Lalle, wani annabi mai girma ya bayyana a cikinmu,” da kuma, “Allah ya kula da jama'arsa.”

17. Wannan labarin nasa kuwa ya bazu a dukan ƙasar Yahudiya da kewayenta.

18. Sai almajiran Yahaya suka gaya masa dukan abubuwan nan.

19. Sai Yahaya ya kira almajiransa biyu, ya aike su gun Ubangiji yana tambaya, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?”

20. Da mutanen nan suka isa wurinsa, suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne ya aiko mu gare ka, yana tambaya, ‘Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?’ ”

21. Nan take Yesu ya warkar da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cuce-cucensu da kuma baƙaƙen aljannu. Makafi da yawa kuma ya yi musu baiwar gani.

Karanta cikakken babi Luk 7