Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 7:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan da Yesu ya ƙare jawabinsa duka a gaban jama'a, ya shiga Kafarnahum.

2. To, sai bawan wani jarumi, wanda Ubangijinsa yake jin daɗinsa, ya yi rashin lafiya, har ya kai ga bakin mutuwa.

3. Da jarumin ɗin ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu shugabannin Yahudawa wurinsa, su roƙe shi ya zo ya warkar da bawa nasa.

4. Da suka isa wurin Yesu sai suka roƙe shi ƙwarai suka ce, “Ai, ya cancanci a yi masa haka,

5. don yana ƙaunar jama'armu, shi ne ma ya gina mana majami'armu.”

6. Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya matso kusa da gidan, sai jarumin ɗin ya aiki aminansa wurinsa su ce masa, “Ya Ubangiji, kada ka wahalar da kanka. Ban ma isa har ka zo gidana ba.

7. Shi ya sa ban ga ma na isa in zo wurinka ba, amma kă yi magana kawai, yarona kuwa sai ya warke.

8. Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.”

9. Da Yesu ya ji haka, ya yi mamakinsa, ya kuma juya ya ce wa taron da suke biye da shi, “Ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.”

10. Da waɗanda aka aika suka koma gidan, suka sami bawan garau.

11. Ba da daɗewa ba, Yesu ya tafi wani gari, wai shi Nayin, almajiransa da kuma babban taro suka tafi da shi.

12. Ya kusaci ƙofar garin ke nan, sai ga wani mamaci ana ɗauke da shi, shi kaɗai ne wajen uwa tasa, mijinta kuwa ya mutu. Mutanen gari da yawa sun rako ta.

Karanta cikakken babi Luk 7