Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 6:32-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. In masoyanku kawai kuke ƙauna wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma suna ƙaunar masoyansu.

33. In kuma sai waɗanda suke muku alheri kawai kuke yi wa alheri, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma haka suke yi.

34. In kuma sai ga waɗanda kuke tsammani za su biya ku ne kuke ba da rance, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma, sukan ba masu zunubi rance, don a biya su daidai.

35. Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama 'ya'yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye.

36. Ku kasance masu tausayi kamar yadda Ubanku yake mai tausayi.”

37. “Kada ku ɗora wa kowa laifi, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yi wa kowa mugun zato, ku ma ba za a yi muku ba. Ku yafe, ku ma sai a yafe muku.

38. Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.”

39. Ya kuma ba su wani misali ya ce, “Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Ashe, dukansu biyu ba sai su fāɗa a rami ba?

40. Almajiri ba ya fin malaminsa. Amma kowa aka karantar da shi sosai, sai ya zama kamar malaminsa.

41. Don me kake duban ɗan hakin da yake a idon ɗan'uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba?

Karanta cikakken babi Luk 6