Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 5:28-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Sai ya bar kome duka, ya tashi ya bi shi.

29. Sai Lawi ya yi masa ƙasaitacciyar liyafa a gidansa, akwai kuwa taron masu karɓar haraji da waɗansu mutane suna ci tare da su.

30. Sai Farisiyawa da malamansu na Attaura suka yi wa almajiransa gunaguni suka ce, “Don me kuke ci kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

31. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da magani, sai dai marasa lafiya.

32. Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi, su tuba.”

33. Sai suka ce masa, “Almajiran Yahaya suna azumi a kai a kai, suna kuma addu'a, haka kuma almajiran Farisiyawa, amma naka suna ci suna sha.”

34. Sai Yesu ya ce musu, “Wato kwa iya sa abokan ango su yi azumi tun angon yana tare da su?

35. Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.”

36. Ya kuma yi musu misali, ya ce, “Ba mai tsage ƙyalle a jikin sabuwar tufa ya yi maho a tsohuwar tufa da shi. In ma an yi, ai, sai ya kece sabuwar tufar, sabon ƙyallen kuma ba zai dace da tsohuwar tufar ba.

37. Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai sabon ruwan inabin ya fasa salkunan, ya zube, salkunan kuma su lalace.

38. Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna.

39. Ba wanda zai so shan sabon ruwan inabin bayan ya sha tsohon, don ya ce, ‘Ai, tsohon yana da kyau.’ ”

Karanta cikakken babi Luk 5